Arewa Blog Top
Alhamdulillah. A calm space for people who love city lights, motivation, and real-life psychology.
A collection of cinematic city videos and photos from Chicago, New York, and Los Angeles — mixed with short, powerful messages about mindset, life, healing, and growth.
29/07/2026
Lallai talauci masifane, ya Allah ka rabumu da talauci Dan tsarkin sunayan ka.
29/07/2026
🚨 REMI TINUBU: "BAI KAMATA WANI ƊAN NAJERIYA YA KWANA DA YUNWA BA"
Uwargidan Shugaban Ƙasa, , ta bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Ta bayyana hakan yayin rabon kayan abinci ga marasa galihu a Akure, Jihar Ondo, inda matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, , ta wakilce ta.
A cewarta, gwamnatin za ta ci gaba da faɗaɗa shirin Renewed Hope Initiative (RHI) tare da kafa bankunan abinci na al'umma domin tallafa wa marasa ƙarfi da kuma inganta lafiyar yara.
Ta ce:
«"Babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya kwana da yunwa. Wannan shi ne manufarmu kuma wani ɓangare ne na hangen nesa na shirin Renewed Hope Initiative."»
💬 A ganinku, shin irin waɗannan shirye-shiryen tallafin abinci za su taimaka wajen rage yunwa a Najeriya, ko akwai wasu matakan da s**a fi dacewa?
29/07/2026
YANZU YANZU:' "Na rantse da Allah Kwankwaso bai taɓa cewa in tsayar da ɗansa takarar mataimakin gwamna ba".-In ji Shugaban Jam'iyyar NDC na Jihar Kano, Hussaini Isah Mairiga.
Me zaku ce?
Wai lokacin da take lalibu abun nashi ina hankalin shi yake 🤣
29/07/2026
Wannan itace sarauniyar a cire duka kowa ya rasa gaba ɗaya, mun jinjina miki sarauniyar wanzaman kasar Hausa🤣🤣
28/07/2026
⚖️ TSAGIN ATIKU: KOTUN ƊAUKAKA ƘARA TA TABBATAR ADC ZA TA SHIGA ZAƁEN 2027
Tsagin jam'iyyar ADC da ke goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, , ya bayyana cewa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ya tabbatar da cewa jam'iyyar ADC za ta shiga zaɓen shekarar 2027.
A cewar sanarwar da ofishin yaɗa labaran Atiku ya fitar, hukuncin ya soke wani hukuncin babbar kotu da ya shafi matsayin ADC da wasu jam'iyyu, tare da kawar da duk wani shingen doka da zai hana jam'iyyar shiga zaɓe.
Sanarwar ta kuma ce wani hukuncin kotu da ya tabbatar da shugabancin kwamitin zartarwa na ADC ƙarƙashin jagorancin ya taimaka wajen kawo ƙarshen takaddamar shari'a kan shugabancin jam'iyyar.
💬 A ganinku, shin wannan hukunci zai ƙara wa ADC ƙarfin siyasa gabanin zaɓen 2027?
27/07/2026
TIRKASHI:" Hakika babu Wanda nake Tausayawa a cikin yan Film's din da s**a bi Mugu kamar Lawan Ahmad, Lawan Ahmad yasamu dama Sosai yayi Wahala ya tara Masoya Mabiya yana harkar Series dinsa.
Kawai ya Tsalle yabi Rarara Yanzu duk Mabiya da Masoyansa daya bata Shekara da Shekaru yana Nemansu Yanzu yayi Losing dinsu da yawa Sabida bin Mugu da yayi a Karshe ina Kiransa da duk yacce zaiyi yayi kada ayi harkar nan a Gama Bai samu a Kalla koda 200M ba.
Saqon Adam A Zango Zuwaga Chairman din Kungiyar Dauda kahutu Barara Triple R wacce take Tallan Dan Takara komai muninsa Indai zai basu Kudi.
Shin Kuna ganin abun da Adam a zango ya fada hakane, Kuma Kuna ganin lawan Ahmad ze iya daukan shawaran da Adam a zango ya bashi.
Ku fada MANA RA'AYIN KU a comment section 👇👇👇
27/07/2026
TIRKASHI:' Sanata Rufa'i Sani Hanga ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
Ya zuwa yanzu dai babu cikakken rahoto kan maƙasudin ganawar tasu.
Amma dai masu nazari na ganin ganawa ce irin ta siyasa duba da taƙaddamar da ke tsakanin Hanga da Kwankwaso.
ME ZAKU IYA CEWA?
27/07/2026
DA ZAFI ZAFIN TA:' Yãɲ binḍiģa sun yi ģarķuwa da wani Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari'a Faruƙu Hassan Bunza.
ME ZAKU IYA CEWA?
27/07/2026
BABBAN MAGANA:" Ƴar Najeriya Mazauniyar Ƙasar Kanada Ta Wallafa Saƙon Murnar Mutuwar Surukarta A Facebook Tare Da Bayyanata A Matsayin "Muguwar Mayya"
Wata Ƴar Najeriya mazauniyar Ƙasar Kanada, Annabiya Ezinne Nwanorue, ta jawo cece-kuce bayan da ta wallafa saƙo a Facebook tana murnar rasuwar surukarta, Comfort Chika Nwanorue, inda ta zarge ta da kasancewa "muguwar mayya."
Lamarin ya haddasa martani mabambanta, inda mutane da dama s**a soki yadda ta yi murnar mutuwar surukar tata, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Ezinne ta shahara a baya-bayan nan a shafukan sadarwa na zamani tana tilasta wa mijinta, Franklin Nwanorue, yin rantsuwar cewa Allah Ya ɗauki ransa idan ya ci amanarta bayan ya isa Kanada. Daga bisani kuma ta yi zargin cewa mijin nata ya karya wannan rantsuwa ta hanyar yin hulɗa da wata mace.
Har zuwa lokacin wallafa rahoton, mijinta da sauran iyalan ba su fitar da wata sanarwa kan sabon lamarin ba.
Shi a ganin ku meyasa wannan matar take murna da mutuwar surukar ta.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Telephone
Website
Address
Kano
Kaduna