Sirrin Cikin Jiki
Sirrin Cikin Jiki 🧠💊
Health tips & body secrets explained simply
Daily videos 🎥
⚠️ For education only, not medical advice
03/10/2026
"Kamar ana hura wuta a cikin ƙafata", ana yawan yi wa likita wannan ƙorafin.
To ko mene ne dalilin?
Daga jin ƙorafin kawai likita ba zai iya ayyana takamaiman dalilin ba. Sai dai, akwai wasu lalurorin da suke da alaƙa da wannan ƙorafin.
Lalurorin sun haɗa da:
1. Lahanin jijiyoyin laka daga ciwon suga.
2. Danne jijiyoyin laka daga ƙasusuwan gadon baya.
3. Lahanin jijiyoyin laka daga raunuka.
4. Ƙarancin sinadarin bitamin B12.
5. Toshewar jijiyoyin jini.
6. Ciwon sikila.
7. Lalurorin fata, kamar cin ruwa, da sauransu.
To wanne ne ba wanne ne ba?!
Gane takamaiman dalili da kuma hanyar magani sadidan sai an zo asibiti, sannan likita ya yi bincike.
02/10/2026
🥕 Karas (carrot) na da muhimmiyar rawa wajen lafiyar jikin mutum, musamman saboda yana ɗauke da beta-carotene, fiber, potassium da sauran sinadarai masu amfani.
Muhimman amfanin karas:
1. 👁️ Yana taimakawa lafiyar ido – beta-carotene na taimakawa jiki wajen samar da bitamin A.
2. 🛡️ Yana tallafa wa garkuwar jiki – bitamin A da sauran antioxidants suna taimakawa aikin kariyar jiki.
3. ❤️ Yana taimakawa lafiyar zuciya – fiber da potassium na daga cikin sinadaran da ke taimakawa lafiyar zuciya.
4. 🌿 Yana taimakawa narkewar abinci – fiber yana taimakawa hanji da samun bayan gida cikin sauƙi.
5. 🧬 Yana ɗauke da antioxidants – suna taimakawa kare ƙwayoyin jiki daga lalacewar oxidative.
6. ⚖️ Yana da ƙarancin calories – yana iya zama wani zaɓi mai kyau a cikin tsarin cin abinci mai kyau.
7. 🦴 Yana taimakawa lafiyar jiki gaba ɗaya – saboda yana ɗauke da wasu bitamin da ma’adanai masu muhimmanci.
Lura: Cin karas yana taimakawa samun sinadarai masu amfani, amma ba ya maye gurbin magani ko cikakken tsarin abinci mai gina jiki.
01/10/2026
Ka san me ke janyo maƙoƙo?
A turance, ana kiranta da "goitre", a yayin da a Hausa kuma ake kiran ta da maƙoƙo. Lalura ce da take bayyana sakamakon kumburin jakar tairod da ke gaban wuya, wato "thyroid gland".
Lalurar tana faruwa sababin ƙarancin ko ƙanfar sinadarin ayodin, wato "iodine" a cikin cimaka. Haka nan, tana iya faruwa sababin kansa / daji da dai sauransu.
Ana magance ta da magunguna ko kuma tiyata idan yin hakan ya zama tilas.
01/10/2026
FITSARINKA NA IYA FADAN SIRRIKAN LAFIYA DA BAKA SANI BA
Ga 3 daga ciki 👇👇👇
01/10/2026
ME YA SA BAKINKA KE WARI DA SAFE.
Ga dalilai 3👇👇👇
30/09/2026
Yana zargin matarsa wai yaron su ba nasa ba ne, shi ne ta turo masa wannan hoton.😀
30/09/2026
Yadda zaka kare kanka daga tsutsar ciki👇👇👇
🚨 WANNAN SAƘO NE MAI MUHIMMANCIN GASKE GA KOWANE ƊAN AREWACIN NIGERIA — YAKAMATA KA KARANTA!
Diphtheria (Mashako) cuta ce mai matuƙar hatsari ga rayuwa, kuma tana haddasa mace-mace tsakanin yara a Katsina da wasu jihohin Najeriya.
Yayin da makarantu ke komawa, muna kira ga iyaye da masu kula da yara da su ɗauki matakan kariya, tare da tabbatar da cewa an yi wa yaransu rigakafin Diphtheria (Mashako) da sauran cututtukan da rigakafi ke karewa.
💉 Rigakafi kyauta ne, amintacce kuma yana da tasiri.
Kare ɗanka yau.
Wannan saƙo ne daga Hukumar Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Ƙasa , da abokan hulɗarta.
30/09/2026
Har yanzu ana yi wa jarirai gashin cibiya kuwa? Saboda na ji wata tsohuwa tana cewa "yaran yanzu ba sa jin magana saboda ba a gasa musu cibiya"😅
30/09/2026
Yadda za ka bambance zazzabin malaria ne ko taifod ke damunka. 👇👇👇
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Sirrin Cikin Jiki posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.