Zauren manema Aure
Kaduna
30/07/2026
"Na yi wa saurayina hidima tsawon shekaru 6, amma ya auri wata cikin wata guda da s**a haɗu."
Wata budurwa ta bayyana cewa ta shafe shekaru shida tana soyayya da saurayinta. Ta ce ta kasance tana mara masa baya a lokacin da ba shi da aiki, tana taimaka masa da kuɗi da kuma ƙarfafa masa gwiwa.
A cewarta, bayan rayuwarsa ta fara daidaituwa, sai ya fara rage mata kulawa. Bayan 'yan watanni kaɗan, ta samu labarin cewa ya yi aure da wata budurwa da ya haɗu da ita ba da daɗewa ba.
Ta ce har yanzu tana mamakin abin da ya sa aka manta da duk irin sadaukarwar da ta yi a tsawon shekarun da s**a gabata.
🔥
Idan ka kasance tare da mutum shekaru da yawa kana taimaka masa, shin hakan yana nufin dole ne ya aure ka? Ko kuwa kowa yana da 'yancin zaɓar wanda yake so?
Ku bayyana ra'ayoyinku cikin mutunci. 👇💬
"Sanin cuta rabin magani" Inji hausawa
Maimuna fa tanason savis 😂
04/07/2026
SABOWAR SHAWARA MAI MAANA DAGA SARKIN ZAZZAU KAN YAWAN HIDINDIMUN AURE...
Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya shawarci iyaye su gargaɗi ƴaƴansu da su guji almubazzaranci wajen kashe kuɗaɗe kan kwalliya da aso-ebi a lokacin bukukuwan aurensu.
Da yake jawabi a bikin cika shekaru 20 da kafuwar Crystal Muslim Organisation (CMO) a Abuja ranar Lahadi, sarkin ya ce ya kamata a karkatar da irin waɗannan kuɗaɗe wajen taimaka wa mabuƙata ko kuma a ba ƙungiyoyin da ke tallafa wa talakawa.
Ya nuna damuwarsa cewa duk da matsin tattalin arzikin da ake fuskanta a ƙasar, iyalai masu hali da dama na ci gaba da kashe maƙudan kuɗaɗe kan abubuwan more rayuwa na alatu, alhali suna yin watsi da buƙatun talakawa. Ya ce wannan na daga cikin abubuwan da ke ƙara haifar da munanan ɗabi’u a cikin al’umma.
Ya ce, “Za ka ga mutane suna kashe miliyoyin Naira kan kayan kwalliya kawai idan za a yi wa yarinya aure, ko kuma su sayi aso-ebi na Naira dubu 500, ko dubu 200, ko dubu 300. A ganina, wannan ba abin karɓa ba ne.”
Ya ƙara da cewa, “Akwai mutane da dama a kan tituna da ba sa iya samun abinci sau uku a rana. Wannan matsala ta yi ƙamari a cikin al’ummarmu. Amma wasu daga cikinmu mun ɗauki matsaya.”
“Ni kaina, ban taɓa kashe ko sisi ɗaya wajen sayen aso-ebi ko kayan kwalliya ga yarinyar da za ta yi aure ba. Idan mahaifiyarta ta ga dama ta yi hakan, wannan ruwanta ne. Ko duk wanda yake so ya yi hakan, ya yi, amma ni ba zan kashe ko sisi ɗaya a kan haka ba.”
Ya ci gaba da cewa, “Ana kashe kuɗaɗe masu yawa a kan bukukuwa waɗanda ba su da wani amfani sosai. Ba na cewa kada a yi biki, amma akwai abubuwan da ya kamata mu rage.”
“Dole ne mu faɗa wa kanmu gaskiya. Ba ma buƙatar irin waɗannan abubuwa, idan aka yi la’akari da halin da ƙasar ke ciki a yanzu.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda haka ina roƙon ku da ku mai da hankali kan abubuwan da za su inganta rayuwarku, su sa ku dogaro da kanku, kuma su ƙarfafa haɗin kai a cikin al’umma.”
“Domin idan kai kana rayuwa cikin jin daɗi, alhali mutanen da ke kewaye da kai ba sa iya samun abinci sau uku a rana, to ina ganin akwai matsala. Wannan ne kuma ke jefa al’ummarmu cikin haɗari.”
Sarkin ya kuma yi kira da a haɗa koyar da sana’o’i a cikin manhajojin makarantun boko da na addinin Musulunci domin ɗalibai su samu damar dogaro da kansu bayan sun kammala karatu, tare da kafa ƙananan sana’o’i daga abin da s**a koya.
Haka kuma, ya buƙaci matasa a faɗin ƙasar da su rungumi fasaha da zamani domin inganta rayuwar al’umma.
Ya kuma roƙi shugabannin siyasa da su dawo da shirye-shiryen bayar da guraben karatu domin taimaka wa masu buƙata su samu ilimin da iyayensu ba za su iya ɗaukar nauyinsa ba.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙasa na Crystal Muslim Organisation (CMO), Alhaji Muhammad Sagir Shettima, ya ce an shirya taron ne domin bikin cika shekaru 20 da kafuwar ƙungiyar wajen yaɗa koyarwar Musulunci da kuma taimaka wa mabuƙata.
Ya ƙara da cewa, a yayin taron an kuma karrama ɗalibai 12 da s**a yi fice a gasar rubutun muƙala ta ƙungiyar, inda aka ba su kyaututtukan kuɗi daban-daban.
Ya yi kira ga Musulmi da su ƙara bayar da sadaka domin tallafa wa talakawa, yana mai cewa ƙungiyar na ba da taimako ga mabuƙata, amma tana buƙatar ƙarin goyon baya domin ta samu damar kai taimako ga mutane da yawa.
Assalamualaikum
Muna Neman Budurwa ko bazawara wadda bata taba haihuwa ba baka wacce ta shirya Aure Daga yanzu zuwa azumi.
Babu Wasa, Kano ko Kaduna
yayiman magana ta wannan number
08036736239
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kaduna
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Zauren manema Aure posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.