USTAZ AHMAD GARBA
To create positive awareness for all mankind, and to make a conducive inviroment to our young youths the leaders of tomorrow
22/08/2026
TALAKAWA IN SHA ALLAHU TALAUCIN FANSA GA AL'JANNAH
Ka daina hassaluwa kana maganganu na sabon Allah dan Allah yayi ka talaka in shaa Allahu iya wahalan kenan, kubi Allah ku daina ruduwa da duniya
Malamin mu ya taba bamu labarin cewa wani malami yana cikin koyar da daliban sa a majalisi, sai s**a ce mlm ka roka mana Allah ya yaye mana talauci
Sai mlmin ya ce bazaiyi hakan ba, s**a ce ko me dalili sai ya ce to in aka yaye masu talaucin sai a baiwa uban waye ya ce kuyi hakuri kubi Allah in sha Allahu karshen wahalar kenan in Allah ya yarda ?
Sai ya karanto masu wannan hadisin
عن ابن عباس قال: قال محمد ﷺ: «اطلعت في الجنة فرأيت أكثر أهلها الفقراء، واطلعت في النار فرأيت أكثر أهلها النساء».
Daga dan abbas ya ce annabi صلي الله عليه وسلم y ce Allah ya hasko min al'jannah, koda na duba sai naga mafiya yawancin cikin ta talakawa ne, sai aka hasko min cikin wuta ( jahannama ) sai naga mafiya yawan cikin ta mata ne.
MATO WANNAN HADISIN DA BAN TSORO YASA ALLAH YASA KU KUBUTA
AHLUL QUR'AN
UTi this guy is doing a very wonderful job, may Allah reword him with jannatul firdaus
22/07/2026
KO MAKARYACI NE JAI KO DAN
Duk wanda ya ce an'yi duniya dan manzon Allah صلي الله عليه وسلم, to tambayan shine inji wa ? in ka ce Allah ne ya fada wallahi kayi wa Allah karya,
To ga gargadi
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًاۚ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ یُعۡرَضُونَ عَلَىٰ رَبِّهِمۡ وَیَقُولُ ٱلۡأَشۡهَـٰدُ هَـٰۤؤُلَاۤءِ ٱلَّذِینَ كَذَبُوا۟ عَلَىٰ رَبِّهِمۡۚ أَلَا لَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّـٰلِمِینَ
In kuma ka ce manmanzon Allah ne ya fada to kai dan wuta ne dan ka jigina masa karya hadisine kuma ingantatacce in ka karyata wata wutan ta karu, ga hadisi kamar gaka
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «مَنْ كَذَبَ عَلَيَّ مُتَعَمِّدًا فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ».
Wannan shine gaskiyar magana, Allah ya raba mu da kirkiran karya mu jingina masa ko ga annabi صلي الله عليه وسلم
KO DA MAGANA NE ?
14/07/2026
Duk wanda ya yi mana sharri ko ya jingina mana maganar da bamu faɗa ba, wai muna cewa Annabi Muhammad ﷺ ba shi da albarka, muna bayyana cewa wannan ƙarya ce kuma ƙazafi ne.
Mu muna ƙaunar Manzon Allah ﷺ, muna girmama shi, kuma muna tabbatar da falalarsa da albarkarsa kamar yadda Alƙur'ani da Sunnah s**a tabbatar.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki: idan wanda ya yaɗa wannan magana mai neman shiriya ne, Allah Ya shirye shi zuwa ga gaskiya.
Idan kuma ya ƙi gaskiya yana zalunci da ganganci, ALLAH YA ISA, domin shine Mafificin mai hukunci tsakanin bayi.
Hasbunallāhu wa ni‘mal-Wakīl.Allah ya haɗa zukatan Musulmi a kan gaskiya, ya nisantar da mu daga ƙarya, ƙazafi, da haifar da fit!na🤲
✍️Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph
13/07/2026
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oon, Allah Ya yi wa Hafiza Bahijjah Adam rasuwa. 😭😭😭
An tabbatar da rasuwar HAFIZA Bahijjah Adam ƴar asalin garin Kaduna, lamarin da ya jefa iyalai, abokai da al'ummar Musulmi cikin alhini.👍👍👍
Marigayiyar ta kasance daga cikin masu hidima ga Alƙur'ani mai girma, kuma ta bar kyakkyawan tarihi na sadaukarwa wajen karatu da koyar da Alƙur'ani.
Muna rokon Allah ya jikan ta kuma ya lullubeta da rahana yasa kabarinta wani yanki ne da al'jannah yasa qur'ani ya ceto ta gobe kiyamah 🙏🙏🙏
Ahlul Qur'an TV
Hukuncin izgili ga wanda yayi shiga irin ta manzon Allah s a w
Tatsinawa
11/07/2026
SAQO ZUWA GA SU 'YAN IYA
Wai sai kaji malami yana cewa a cigaba da karatu a daina radde radden nan, ayyaa mlm ka bani tausayi sai ka ce baka karanta qur'ani ko littatafan magabata ko dai so kake ka nuna wani bai iya ba sai kai ?
Qur'ani shine kundi kuma cike ake da raddi to yaya kenan ? mlm abinda yakamata ka fada shine a daina cin mutuncin ko taba shaksiyya a yayin yi ko mayar da raddi,.
Ah shikenan dan kai kana wa'azin kar a zage ni shine wancan nashi ba daidai yake ba , ko baida usulubi malamai aji tsoron Allah kar garin kushe wani ka kushe qur'anin baki daya
Shin yanayin usulubin sayyidaina umar ko fahimtar sa daya yake da na sayyidaina abubakar ko na sayyidaina Ali daya yake da sayyidaina uthman kai a dole sai ka mayar da kowa ya zama kai ina zai yu ??
Kayi iya naka yayi iya nashi suyi iiya nasu nayi iya nawa abinda Allah ke karba shine wanda yayi dan Allah shiyasa Allah ya ce
إِنَّمَا یَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِینَ
وَٱلۡعَـٰقِبَةُ لِلۡمُتَّقِینَ
ALLAH KA KARA MANA IKHLASI
Click here to claim your Sponsored Listing.