Shaheed Ahmad Zakzaky

Shaheed Ahmad Zakzaky

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Shaheed Ahmad Zakzaky, Health/Beauty, Abuja.

15/09/2026

بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ

"مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيْهِ ۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُ ۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبْدِيلًا"

Cikin alhini da juyayi muke miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga Sahibul Asr (Ajjalallah Farajahu Sharif), da jagoran mu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).

Na Rashin; Marhum Muhammad Abdullahi

Yau Talata: 15/09/2026. Yayi dai dai da kwana uku na rasuwar: Marhum Muhammad Abdullahi

Marhum ya kasance jajirtaccen ɗan uwa mai sallamawa da jajircewa, k*ma hazikin matashi mai himma wajen kula da addini, sannan ya kasance cikakken ma'aikaci a cikin matasa na rundunar Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky (JASAZ) a Zone ɗin Mukhtar Assakafy, k*ma mai bada gudunmawa da himma wajen sauke nauyin da ke kansa.

Ya rasu a ranar Lahadi. 13/09/2026, sak**akon accident da ya ritsa dashi akan hanyar dawowa Muzahara a garin Wurno zuwa Achida wanda anan ya cimma wa'adin sa.

Muna ƙara miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyaye, abokai da ƴan uwansa, Allah ya girmama matsayin sa ya karɓi uzurinsa, ya sadashi da Shahidan Muslumci.

Muna roƙon ƴan uwa da su sanya shi cikin addu'oin su tare da barar Fatiha daya, da Salatin Annabi goma sadaukarwa zuwa ga ruhin sa.

KULLU NA AHMAD YA ABA AHMAD

JASAZ Shuhada Department.
15/09/2026.

14/09/2026

Shirin Bahasin Makon Shaheed Ahmad Zakzaky Na Shekarar Data Gabata (2025)

Kasance tare da Fa'eez Media domin jin bahasin Makon Shaheed Ahmad Zakzaky na shekarar data gabata (Ahmad Week 2025) wanda zamu đora muku shi a shafinmu na YouTube a karshen makon nan da muke ciki.

10/09/2026

JAGORA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H): TURAWAN YAMMA NA AMFANI DA RARRABUWAR KAI WAJEN KWASHE ARZIKIN NAJERIYA

Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya ƙara da cewa, wannan salo ne da ya ce Turawan Yamma ke amfani da shi wajen haddasa rigingimu a Najeriya, yayin da suke kwashe arzikinta ta hanyar amfani da wasu ruɓaɓɓun shugabannin siyasa waɗanda ke yi musu aiki.

Wannan wani ɓangare ne daga jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na rufe Mu’utamar na Dandalin Matasan Fulani (Sukabe Shehu Baba Julbe), karo na uku, a Abuja.

19 ga Rabi’ul Auwal 1448AH | 01 September 2026

09/09/2026

Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ya ce: “Kuma wannan al’umma da muke a ciki, lallai tana buƙatar waɗanda za su sadaukar ne, su tsaya kyam a tafarkin Allah har al’amari ya dawo daidai. Kuma in ba haka nan ba, an dinga fuskantar irin abin da ake fuskanta kenan, na wahaloli; wannan ya bullo bayan wani.”

—Bangaren Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A Mu'utamar Amm Bauchi a Shekara ta 1447/2026.

Mahadee Musa Aliyu | ABS Radio Hausa

07/09/2026

AN JARABCI ZUKATAN MUMINAI ’YAN GWAGWARMAYA A DUNIYA

Jarabawa ta tsananta, Shahidai sun yi shahada, amma imanin ’yan gwagwarmaya bai raunana ba. A maimakon haka, shahadarsu ta ƙara ƙarfi, izza da jajircewa wajen ci gaba da gwagwarmaya.

JERIN SHAHIDAI

Shaheed Qassem Soleimani & Abu Mahdi Al-Muhandis
A Rabar 03 January 2020

Shaheed Ibrahim Raisi
A Ranar 19 May 2024

Shaheed Sayyid Hassan Nasrallah
A Ranar 27 September 2024

Shaheed Ayatollah Sayyid Ali Al-Khamene’i (H)
A Ranar 28 February 2026

Shaheedai Daliban Makarantar Minab
A Ranar 28 February 2026

Shaheed Ali Larijani
A Ranar 17 March 2026

SAƘON YAN GWAGWARMAYA

Duniyar gwagwarmayar ta tashi tsaye da karfi tare da slogon, Mutuwa ga Amurka da Isra'ila.

Shahidai sun tafi, amma gwagwarmaya tana nan daram, Hawaye basu karya gwiwar Yan gwagwarmaya ba, jarabawar ta ƙara karfi a zukatan yan gwagwarmaya ta cigaba da tafiya da Juriya, Hakuri, Hadafi nanan Daram akan abinda suke akai na shafe zalunci da azzaluman duniya.

Gwagwarmaya za ta yi nasara, Insha Allah🚩✊

— Muhammad Baqeer
06/September/2026

07/09/2026

“FADA DA AL’UMMAR MUSULMI FADA DA MUSULUNCI NE.” — JAGORA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

Sheikh Zakzaky (H) ya ce: “Kun san Lakurawan nan da akwai lakurawan gari dana daji. Da, mun dauka a daji ne kawai sai da muka ji na gari suna ta kyarara kyarara, muka ce ashe lakurawan suna da yawa. Karku ce muna makon hadin kai na ware lakurawa, muna so lakurawan su dena mene? Lakuranci.

“Fada da musulmi bazai taimake ku ba, fada da al'ummar musulmi fada da Musulunci ne, wannan ba dubara bane. Sai s**e wai sai an tsarkake gida kafin ai kaza, su da dan uwansu musulmi zasu yi fada. Banda wannan k*m sai s**a shigo mana da rarraba na addini, banda an addini ma s**a shigo mana dana Kabila, dana bangare, duk ana jefo mana, su k*ma mutane suna ta fadawa.

“Da yake nasan cewa k**ar yadda nace muku wasu ‘Business ne fa’ ana samu ne, yanzu zaka ga anba mutum kudi, yaita banbami yana zage-zage a biya shi—yaci gajiyan zagi din. To, wannan dai abinda zamu ce musu shi ne wannan al'umma wajibinta ne ta farka k*ma zata farka din.“

—Bangaren Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na rufe taron Makon Haɗin Kai na bana, a gaban dimbin al’umma Musulmi, a ranar Lahadi, 17 ga Rabi’ul Auwal, 1448H, a Abuja.

–Mahadee Musa Aliyu | ABS Radio Hausa

07/09/2026

Gayyata!

Jaishu Shaheed Ahmad Zakzaky, Firqatu Shaheed Humaid na farin cikin gayyatar yan uwa zuwa wajen taron tunawa da ranar haihuwar Shaheed Humaid wanda zai gudana k**ar haka:

Rana: Lahadi, 24th Rabi'ul Awwal, 1448 - 6th September, 2026
Lokaci: Karfe 10 Na Safe
Muhalli: Abuja, Nigeria

Allah swt ya bada ikon halarta

Sanarwa: JAFSH Media

06/09/2026

“JA-INJA DIN KUDU DA AREWA YA DAUKE HANKULAN MUTANE.” — JAGORA SAYYID IBRAHEEM ZAKZAKY (H)

Sheikh Zakzaky (H) ya ce: “Su k*ma makiya sai s**a yi wani tunani na kawo mana rarraba wanda zai hana mu ma tunani, aka kawo mana rigiman bangaranci—aka ce mana sunanmu Kudu da Arewa, anata rigiman Kudu da Arewa, ja-inja din Kudu da Arewa ya dauke hankalin mutane kwarai da gaske na tsawon lokaci.

“Sannan k*ma bayan rigiman Kudu Arewan, aka zo ko wanne a ciki aka bashi bangarancin, Kudun ma nada bangarori, Arewan ma nada bangarori. Sannan k*ma aka zo aka bamu wata mahanga ta daban na addinai, akace sunanmu Musulmi da Kirista. Aka sake zuwa aka bamu wata mahangar daban, akace sunanmu Kabiloli, sunanmu Kabila kaza da Kabila Kaza, harda abinda bai k**ata ma ace akwai shi da sunan Kabila ba, shima an kawo mana, akacw shima sunan Kabila ne.

“Kuma wani rikicin da ya wuce wannan ma a cikin addini din, aka zo akace mana bangare kaza ne da bangare kaza, shima addinin an rarraba shi, akwai yan kaza akwai yan kaza, duk wannan shi ya dauke hankukan mutane.”

—Bangaren Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A Mu'utamar Amm Bauchi a wannan Shekarar ta 1447/2026.

Mahadee Musa Aliyu

05/09/2026

“Ma’aikatan Tsaro Na Ƙasar Nan Cima Zaune Ne.” —Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky(H)

Sheikh Zakzaky (H) ya ce: “Su dama ma’aikatan tsaro na kasar nan cima zaune ne, marasa aikin yi amma masu kwasan albashi, basu aikin komai, basu tsinana ma kasar nan komai sai sharri, amma ana basu albashi. Idan aka sa mutum yai aikin tsaro, ya kawo rahoto, inya dade bai samu aikin yi ba, to sai ya kulla wani sharri ya aika, don ya nuna cewa lallai yana aiki sosai.

“Kamar in ansa shi ya lura da gidan wani ko wani abu na faruwa, sai yace ‘ai wata rana yana lura can tsakan dare sai yaga wata jan mota tazo, wani jan mutum ya fito.’ Nan fa bai ga komai ba, sai yace wa mutane mena gaya muku mutumin nan fa yana hulda da kasashen waje. To, shi kenan, sun saba irin wadannan abubuwan suna yi.“

—Bangaren Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), bayan k**a shi a filin jirgin sama (Airport) na Kano zashi Ingila a shekarun baya.

—Mahadee Musa Aliyu| ABS Radio Hausa

04/09/2026

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ce: “Duk lokacin da kake magana, su mutane ba sauraronka suke yi ba! Kallon ka suke yi, suga wai a ina zasu aje ka, kai dan menene? Shi kenan abinda ya dame su, basama sauraron abinda kake cewa, komai maganan da kake yi da duk maganan da kayi, da duk hankalin daka kawo, da duka hujjojin daka kawo, duk bashi ya dame su ba, kai dan menene? In kai nasu ne to kayi daidai, abinda ka fada kayi daidai ko ba daidai bane.

“In ba nasu bane k*ma duk abinda ka fada ba daidai bane. In suna da nasu k*ma duk abinda nasun ya fada daidai ne ko ba daidai bane, k*ma in wani bana su bane ko mai ya fada ba daidai bane. Bilhasali ma wasu basama sauraron kowa sai nasu, to wannan duk ayyuka ne da makiya s**a ingizo mana.”

—Bangaren Jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A Mu'utamar Amm Bauchi a wannan Shekarar ta 1447/2026.

—Mahadee Musa Aliyu| ABS Radio Hausa

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Abuja